Kotu zata cigaba da sauraron kara dake kalubantar wa’adin daina karbar tsofaffin kudade a Najeriya

Kotun kolin kasar nan ta sanya ranar 22 ga watan nan na fabrairu a matsayin ranar da zata cigaba da sauraron kara da gwamnanonin jihohin kasar nan suka shigar gabanta dake kalubantar wa’adin daina karbar tsofaffin kudade a wannan kasa.

A zaman ktun na wannan rana rahotanni sunyi nuni da cewa harabar kotun ta cika makil da al’umma cikinsu har da gwamnonin jihohin kaduna Nasir El- rufa’i da kuma na kogi Yahya bello.

A yayin sauraron karar a wannan rana mai sharia john okoro wanda shine ya jagoranci ayarin alkalai 7 dake sauraron shari’ar yace kotun kolin zata maida hankali wajen ganin an bawa dukkanin bangarorin biyu hakkinsu duba da cewa lamarin da ake magana ya shafi al’umma da kuma zaman takewa jingine sauraron karar dai zuwa ranar 22 ga wannan wata.

Wannan dai ya biyo bayan buqatun da wasu karin jihohi suka suka nuna na shiga a dama dasu a shari’ar jihohin na baya bayan nan da suka nuna sha’awar hakan sun hada da jihohin niger da kano da ondo da lagos da katsina da ogun da kuma sokoto sai dai kuma an samu wasu jihohin dake nuna goyon baya ga bangaren gwamnati da suka hada da bayelsa da kuma ekiti

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *