Kotu ta sanya ranar 28 ga Maris a matsayin ranar za ta yanke wa Patience Jonathan hukunci kan zargin rashawa

Babban kotun tarayya da ke jihar Legas ta sanya ranar 28 ga watan gobe a matsayin ranar za ta yanke hukunci akan bukatar da hukumar EFCC ta gabatar na neman mallakawa gwamnati tsabar kudi sama da dalar Amurka miliyan biyar da kuma kudin najeriya sama da naira biliyan 2 mallakin uwargidan tsohon shugaban kasar nan Dame Patience Jonathan.

Alkalin kotun Mai Sharia Tijjani Ringim wanda ya bayyana haka a yayin zaman kotun na wannan rana ta Laraba, ya kuma yi watsi da bukatun da lauyoyin wadanda ke daawar mallakar kudaden suka gabatar wa kotun na neman sake sauraron karar duba da cewar an samu sauyin alkalin da ya fara
sauraron karar kafin kawowa ga wannan mataki.

Hukumar EFCC ta gabatar wa da kotun bukatar a mallakwa gwamnati wadannan makudan kudade ni tun a shekarar 2017 bukatar da alkalin kotun na wancan lokaci mai Sharia Mojisola Olatoregun ya amince dashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *