Gwamnatin jihar Katsina ta janye karar da ta shigar inda ta ke zargin Ibrahim Shehu Shema da Ibrahim Lawal Dankaba da laifin yin sama da fadi da naira biliyan 11

Gwamnatin jihar Katsina ta janye karar da ta shigar gaban babban kotun jihar inda ta ke zargin tsohon gwamnan Ibrahim Shehu Shemada kuma tsohon shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi na jihar Ibrahim Lawal Dankaba da laifin yi sama da fadi da naira biliyan 11 daga cikin kudin
kananan hukumomim jihar.

A cewar daraktan a maaikatar sharia ta jihar Abdulrahman Umar, janye ya karar ya biyo bukatar da gwamnati ta gabatarwa da kotun akan hakan.

Idan dai zaa iya tunawa a shekara ta 2016 ne, gwamnatin jihar Katsina ta gurfanar da tsaffin shubanni biyu a gaban kotu bisa zargin cin amana da zamba da kuma amfani da kudaden alumma ba bisa kaida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *