NACA ta gargadi matasa da su gu ji sharholiyar da za ta iya kai su ga hadarin kamuwa da cutar mai karya garkuwar jiki

Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki(NACA) ta Najeriya ta gargadi matasa da su gu ji
sharholiyar da za ta iya kai su ga hadarin kamuwa da cutar.

Shugaban hukumar da ake kira NACA a takaice, Gambo Aliyu, shi ne ya yi gargadin ga jama’a
musamman matasa, a jiya Litinin.

A sakonsa na ranar masoya da ake kira Valentine’s Day na wannan shekara, shugaban
ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci su yi gwaji domin sanin
matsayinsu dangane da cutar ta HIV/AIDS.

Aliyu ya shawarci matasa da su yi bikin cikin nuna so da kauna da kare masoyansu daga duk wani abu da zai iya cutar da su, sannan su guji aikata abin da zai iya kai su ga kamuwa da cuta
mai karya garkuwari jiki.

A duk shekara rana irin ta yau 14 ga watan Fabarairu ake bikin Ranar Masoya a duniya,
wadda ake kira Valentie’s Day.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *