Kotu Ta Hana Ganduje Korar Muhyi

Kotun Kula Ma’akata ta Kasa ta dakatar da Gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga korar Barista Muhyi Magaji Rimingado daga mukaminsa na Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Rashawa ta jihar.

Wannan ya biyo bayan rokon da lauyoyin Barista Muhuyi Magaji Rimingado suka gabatar a gaban kotun da ke zamanta a Kano, a shari’ar da yake kalubalantar korar da gwamnatin Kano ta yi masa, wadda ya ce ta saba doka.

A zaman kotun na ranar Litinin Lauyan Muhyi, Barista Yusuf Ali Faragai, ya bayyana wa kotun cewa takardar da Gwamnatin Jihar Kano ta bayar a matsayin ta korar wanda yake karewa, a fahimtarsu an yi ta ne ba bisa ka’ida ba.

Faragai ya kara da cewa, tuni suka shigar da kara a Birnin Tarayya Abuja kuma kotu ta tabbatar da Barista Muhuyi Magaji Rimingado a matsayin halastaccen Shugaban Hukumar Karbar Qorafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *