Gwamnatin Jihar Zamfara ta umarci dukkanin kungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a jihar
su tattara su fice ba tare da bata wani lokaci ba.
Umarnin na cikin wata sanarwa ne da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na
jihar Mamman Tsafe ya fitar.
Sanarwar ta zargi kungiyoyin wadanda ba na gwamnati ba da gudanar da ayyukan da ke iya
kara matsalar tsaro a jihar da makwabta.
Gwamnatin ta ce ta lura da yadda kungiyoyin suke ta karuwa a jihar inda suke gudanar da
ayyukan da suka saba wa doka.
Kuma ta ce ta lura yawancin kungiyoyin ba su yi rijista a jihar ba kamar yadda doka ta tanada.
Sanarwar ta umarci ma’aikatu da sassa da kuma hukumomin gwamnati da su daina duk wata
mu’amulla da kowa ce kungiya, tare da gargadin cewa za a hukunta duk wata hukumar gwamnati
da ta yi mua’mulla da kungiyoyin.
Gwamnatin ta kuma bayar da umarni ga hukumomin tsaro da su sanya ido domin gano
duk wata kungiya da ke aiki ba tare da takardar izini daga hukumar da ta dace ba, domin
gurfanar da ita a gaban kotu.