Bankunan kasuwanci sunyi watsi da umarnin kotu, sun shiga jerin masu kin karbar tsofaffin takardun Naira.

Rahotanni na nuni da cewa bankunan kasuwanci sun shiga jerin masu kin karbar tsofaffin
takardun Naira duk da umarnin Kotun Koli.

Kotun Koli ta ba da umarnin tsawaita wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira 1,000 da N500
da N200 da aka sauya zuwa ranar Laraba, 15 ga Fabrairu inda za ta dauki mataki biyo bayan
karar da aka shigar a gabanta.

Rahoton ya kara da cewa an gano yadda wasu bankunan kasuwacin ke kin karbar tsoffin kudin
daga hannun jama’a yayin da suka shiga neman canji a karshen makon da ya gabata a wasu
jihohi, ciki har da Abuja.

Jihohin Legas da Abuja da Kwara da Ondo da Borno da Imo da Binuwai da Edo da Neja da
Ebonyi da Ribas da Oyo da sauransu, na daga cikin jihohin da aka gano bankuna ke kaurace
wa karbar tsoffin kudi.

A yankin Abuja kuwa, daya daga cikin manajojin bankin ya shaida wa wakilinmu cewa sun rufe
wasu sassan bankinsu na Zenith ne saboda rashin kudi.

Lamarin ya shafi har da gidajen mai da manyan kanti kamar yadda bincike Aminiya ya gano.

Domin kuwa wasu gidajen mai wasu sassan
Abuja, da suka ha da NNPCL da ke Berger da
Zone 4; da gidan man Total ke Zone 3 da dai
sauransu, sun daina karbar tsoffin kudi.
Haka ma lamarin yake a Jihar Borno,inda tuni
wasu gidajen mai da kantunan zamani suka
kurace wa karbar tsoffin takardun Naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *