Mai Mala Buni ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa yayin yaƙin neman zaɓe

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai masa yayin yaƙin neman zaɓe a shiyyar Gashua da ke ƙaramar hukumar Bade.

Sai dai gwamnatin jihar Yobe ta musanta Ikirarin tana cewa sai da gwamna ya bar wurin hayaniya ta ɓarke.

Amma gidan Talabijin na ChannelsDubban magoya bayan APC ɗin ne da suka je yakin neman zaɓen suka riƙa yi wa gwamnan ihu suna cewa “ba ma yi, ba ma son Mai Mala Buni”.

An fara rikicin ne lokacin da gwamnan zai miƙa tuta ga ‘yan takarar APC gabanin zaɓen 2023, kawai sai aka fara jifa da dutse da wasu abubuwan na daban.

Sai da aka fitar da Gwamnan daga taron tare da taimakon jami’an tsaro.

Yana yin dai haka ya tilastawa gwamnan da magoya bayansa barin yankin tare da komawa Damaturu ba tare da shiri ba.

Mamman Mohammed wanda shi ne daraktan kula da kafafen yaɗa labari ya
ce babu wani abu mai kama da wannan da ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *