INEC: “Ba za a yi zabe a rumfunan zabe 240 ba”.

Kasa da kwanaki 12 kafin zaben Najeriya, Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, tace ba za a yi zabe a rumfunan zabe 240 ba.

Shugaban Hukumar zaben ta kasa, Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa a ranar Litinin.

Yakubu yace dalilin da ya sa ba za’a gudanar da zabe a rumfunan zaben ba shine, babu wanda ya zabi ya kada kuri’arsa a wadannan rumfunan zaben har zuwa lokacin da aka kammala yin rajistar masu zabe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *