“Fiye da mutum 20 ne ake fargabar sun mutu sanadin cutar sanƙarau da ta ɓulla bana a Jigawa

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce fiye da mutum 20 ne ake fargabar sun mutu sanadin cutar sanƙarau da ta ɓulla bana a jihar.

Jihar Jigawa dai ta yi iyaka da Jihar Damagaram, ta Jamhuriyar Nijar wadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da rahoto a makon jiya cewa mutum 18 sun mutu sanadin cutar ta sanƙarau da ta ɓarke a can.

Hukumomi a jihar Jigawa sun ce tuni suka gudanar da taron gaggawa da Hukumar Daƙile Cutuka ta Najeriya wadda ta yi alƙawarin aika riga-kafi ga mazauna yankunan kan iyaka.

Ga ƙarin bayanin da Dr. Salisu Mu’azu, Babban Sakataren a ma’aikatar lafiya ta Jigawa ya yi:

Ita dai cutar sankarau cuta ce wadda take da hadarin gaske da take shafar kwakwalwa da laka, kuma ta kasance babban kalubale ga duniya .

Kwayoyin baktiriya su ne suka fi haddasa ta.

Dr. Salisu Mu’azu, Babban Sakataren a ma’aikatar lafiya ta Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *