DSS ta gayyaci Femi Fani- Kayode a kan zargin da ya yi cewa ana shirya juyin mulki.

Hukumar tsaro ta DSS ta gayyaci darektan yada labarai a kafafen intanet na kwamitin yakin neman zabe na shugaban kasa a jam’iyyar APC Femi Fani- Kayode a kan zargin da ya yi cewa ana shirya juyin mulki.

A wata sanarwa da ya fitar da safiyar Litinin din nan ne Fani-Kayode ya ce hukumar ta gayyace shi.
Jigon na jam’iyyar APC ya ce zai amsa gayyatar domin babu wani abu da yake jin tsoro.

Kuma ya ce zai ci gaba da bayyana ra’ayi da duk wani abu da ya fahimta in dai har yana raye.

A ranar Asabar ne Fani kayode a wasu sakonni da ya rika sanyawa a shafin Twitter ya ce, ya fahimci cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar

PDP, Atiku Abubakar ya yi wata ganawa da sirri da wasu janar-janar din soji.

Bayan wannan ne kuma sai hedikwatar tsaron Najeriya ta fito ta musanta
wannan taro tana mai jaddada aniyarta ta kare dumukuradiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *