Atiku Abubakar, ya yi kira ga DSS, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro, su kama Femi Fani- Kayode dangane da kalaman da yayi.

Dan takaran kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga DSS, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro, su kama Femi Fani- Kayode dangane da kalaman da yayi.

Atiku Abubakar ya fitar da wannan jawabi ne ta bakin Mai taimaka masa wajen harkokin sadarwa, Phrank Shaibu.

Phrank Shaibu ya fitar da jawabi na musamman a matsayin raddi ga wasu maganganu masu nauyi da Femi Fani-Kayode ya yi a shafinsa.

Da yake magana a dandalin Twitter, Fani-Kayode wanda Darekta ne a kwamitin neman zaben Bola Tinubu, ya ce ana shirye-shiryen juyin mulki.

Tsohon Ministan tarayyar ya zargi Atiku Abubakar da wasu manyan Janar na sojoji da nufin kifar da gwamnati ko kuma su hana yin zabe a Najeriya.

Shaibu ya bayyana cewa tun farko ba su yi niyyar maidawa jigon na APC martani ba domin a ‘yan shekarun nan, ya yi suna a sharara karya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *