“A yanzu na daina yarda da shugabancin Muhammadu Buhari”. – El Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa a yanzu ya daina yarda da shugabancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Idan za a iya tunawa, a ci gaba da sabon shirin sauyin fasalin kudi na baya-bayan nan da Babban Bankin Najeriya, CBN ya yi, gwamnan ya tayar da hankalin cewa wasu daga cikin kusoshin fadar shugaban kasa na yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu zagon kasa.

Gwamnan, wanda ya sha alwashin cewa wadanda ke goyon bayan Tinubu za su yi galaba a kan masu shirya tuggun, yana mai cewa zai yaye fuskokinsu kowa ya gani nan ba da dadewa ba.

El-Rufai ya yi zargin cewa wasu mutane a fadar shugaban kasa da suka marawa wani dan takara baya a lokacin zaben fidda gwani na APC suna amfani da Buhari wajen aiwatar da shirinsu.

Hakazalika, a wata hira da manema labarai, gwamna El Rufa’i ya bayyanan cewa duk da cewar ya yi imani da Buhari, amma ya daina amincewa da wadanda ke tare da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *