EFCC: “Bankunan kasuwanci ne suka janyo tarnaƙi wajen ganin sabbin kuɗi sun wadata a hannun jama’a”.

Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta ce bankunan kasuwanci ne suka janyo tarnaƙi wajen ganin sabbin kuɗi sun wadata a hannun jama’a.

EFCC ta ce bayanai daga Babban Bankin Najeriya sun nuna cewa zuwa yanzu, CBN ya buga sabbin takardun kuɗi sama da naira biliyan 400, amma bankuna sun ƙi fitarwa su bai wa jama’ar ƙasar.

Shugaban hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa a wata tattaunawa da BBC, ya buƙaci ‘yan Najeriya su tona asirin masu ɓoye sabbin kuɗi, don ganin hukumar ta je ta ƙwace su.

Abdurrashed Bawa ya ce wannan ita ce mataki na gaba da suke ganin zai taimaka wajen kawo wa talakan Najeriya waraka.

Sannan ya tunasar da cewa akwai tukuici mai gwabi ga duk mutumin da ya taimaka aka gano wurare ko mutumin da ke rike da sabbin kudade.

Shugaban na EFCC ya ce babu shaka sun yi na’am da wannan sauyi kuɗi, saboda bayanan sirri ya nuna musu cewa akwai mutane da dama da suka boye kuɗaɗe, suna cinikayya a boye.

Sai dai ya ce babbar matsalarsu ita ce ma’aikatan banki, saboda duk da cewa kuɗaɗen da aka buga ba su wadatu ba, ma’aikatan na bai wa wasu mutane kuɗaɗen a ɓoye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *