Shugaba Muhammadu Buhari zai jagoranci wani taron gaggawa na majalisar magabata ta kasar a ranar Juma’a

Shugaba Muhammadu Buhari zai jagoranci wani taron gaggawa na majalisar magabata ta kasar a ranar Juma’a wanda ya kasance ranar da aka sanya wa’adin daina amfani da wasu daga cikin manyan takardun kudin kasar.

Taron zai tattauna ne a kan matsalolin da kasar ke fama da su a yanzu da suka hada da karancin man fetur da na kudin kasar Naira da matsalar tsaro yayin da kasar ke fuskantar babban zabenta da za a fara ranar 25 ga watan nan Fabrairu wato kasa da sati uku daga yanzu.

Halin da kasar ke ciki na wadannan matsaloli musamman karancin Naira da kuma matsalar mai sun sa an fara zanga-zanga a wasu sassan kasar da dama.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ana sa ran gwamnan Babban Bankin Najeriyar, Godwin Emefie zai yi wa majalisar bayani a yayin taron da zai gudana a fadar shugaban kasar, da ke Abuja, game da batun canjin kudin ksara, lamarin da ya jefa al’umma da dama cikin halin kaka-ni-kayi.

Haka kuma jaridar ta kara da cewa wasu kafofi na fadar shugaban sun bayyana cewar shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Mahmood Yakubu, da shugaban.

‘yan sanda na kasar Usman Alkali Baba za su yi wa majalisar bayani kan shirye-
shiryen zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da za a yi ranar 25 ga

watan na Fabrairu da kuma na gwamnoni da ‘yan majalisar jiha da za a yi ranar 11
ga watan Maris.
Majalisar magabatan ta kunshi shugaban kasar da mataimakinsa da sakataren
gwamnatin tarayya da tsofaffin shugabannin kasa da tsofaffin manyan alkalan
kasa da shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai da
gwamnonin jihohi 36 da kuma babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *