Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da CBN daga aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin takardun Naira.

A bayan dai CBN ya saka ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsoffin takardun 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sake.

Jihohin Arewa uku – Kaduna, Kogi da Zamfara – sun shigar da karar a ranar 3 ga watan Fabrairu, inda suka bukaci kotun koli da ta dakatar da yunkurin da gwamnati tarayya ke yi na daina amfani da tsofaffin takardun Naira daga ranar 10 ga Febrairu, 2023.

Lauyan da ya tsayawa jihohin, Mr A. I Mustapha, SAN, ya bukaci kotun ya amince da bukatarsu saboda yanayin da wannan dokar ya jefa al’ummar Najeriya a ciki.

Ya bayyana cewa wannan doka ta gwamnati ya jefa yan Najeriya cikin wahala.

Lauyan ya kara da cewa muddin kotun koli bata shiga lamarin ba Najeriya na iya shiga wani irin hali

A hukuncin wucin-gadin da suka suka yanke, alƙalan kotun bakwai ƙarƙashin jagaorancin mai shari’a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin tarayya da Babban bankin ƙasar da sauran bankunan kasuwanci na ƙasar daga aiwatar da wa’adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.

Kotun ta kuma ce dole ne gwamnatin tarayya da CBN da kuma sauran bankunan ƙasar sun jingine batun aiwatar da wa’adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin ranar 15 ga watan Fabrairu.

saboda bankuna a fadin Najeriya har sun fara rufe ofishohinsu.

One Reply to “Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da CBN daga aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin takardun Naira.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *