Jamb ta soke rijistar dalibai 817 da zasu zana jarabawarta a 2023

Hukumar shirya jarabawar shiga Manyan makarantun gaba da Sakandare ta Kasa wato Jamb ta ce ta soke rajistar dalibai 817 da suka yi rijistar zana jarrabawar ta shekarar 2023.

Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Isiaq Oloyede, a karshen mako ya bayyana cewa kimanin dalibai 789 ne aka soke musu rijistar jarabawar sakamakon karya ka'idojin rijistar.

Shugaban hukumar ya kuma jaddada cewa daliban sun karya dokar rijistar ne ta hanyar, sanya yatsu goma a na'urar daukar hotan zanen yatsa, sai biya masu yin rijistar, su dauki hoton yatsu mutane daban daban ta yadda kowane daga cikinsu zai iya shiga ya zana jarrabawar.

Oloyede ya bayyana cewa: "Inshaa Allah, JAMB na gano su duka, kuma muna da isassun kayan aiki da za mu cigaba da gane su, kuma mu kama su.

"Babu wata gajeriyar hanya na samun nasara a jarabawar UTME, tabbataccen hanya daya na samun nasara ita ce yin karatu da bin ta hanyar da ta dace."Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *