Buhari ya ce zai ci gaba da yi wa Tinubu yakin neman zabe duk da zagon kasa da akeyi masa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da yi wa ɗan takarar jam’iyyarsu ta APC Bola Ahmed Tinubu yakin neman zabe duk da zagon kasa da akeyi masa domin ya gajeshi a matsayin shugaban kasa.

Da yake magana a gaban dubban magoya bayansu a Jihar Nasarawa shugaba Buhari ya ce ya yi imanin Tinubu zai sadaukar da kansa ga Najeriya.

Shugaban yace yasan Bola Tunubu un sama da shekara 20 a dan haka baya tantamar cewa zai kawo sauyi a Najeriya.

Kalaman nasa na zuwa ne kwana biyu bayan wasu jiga-jigai a APC sun yi zargin cewa wasu manya daga cikin jami’an gwamnatin ta Buhari na adawa da takarar Tinubu.

A cewar Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, masu adawar ba sa son APC ta yi nasara ne saboda ɗan takarar da suka mara wa baya a zaɓen fitar da gwani bai yi nasara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *