Akwai yiyuwar daga Gobe Litinin A dakatar da raba man fetur a sassan Najeriya ciki harda jihar Kano .

Wannan na zuwa ne sakamakon Boren da kungiyar masu sayar da man fetur masu zaman kansu na IPMAN ta kasa tayi na cewa muddin gwamnatin tarayya ta tirsasasu sai an sayar da man fetur Akan naira 195 ko wacce lita to kuwa Basu da wata matsaya illa su rufe Gudajen man fetur a Najeriya Kuma
a dakatar da raba shi daga Gobe Litinin.

A wani taro da aka shafe daren Asabar zuwa wayewar garin yau Lahadi anayinsa a Abuja wanda ya hada da Kamfanin NNPC da Hukumar kayyade farashin man fetur da Hukumamomin kula da albarkatun man fetur na cikin ruwa da kan tudu da kungiyoyin dillacin man fetur da sayar dashi,an tsaya kan cewa dole ne a sayar da man fetur Akan Naira 195 maimakon sama da Naira 210 da aka sayar dashi a Gidajen man fetur wasu daga cikin Yan cuwa cuwa Kuma dama da naira 350 duk lita Daya ,inda Kungiyar ta IPMAN tace
ba zata amince ba.

Shugaban kungiyar dilllan man fetur Mai zaman kanta ta kasa IPMAN Com Debo Ahmed yace muddin suka amince da wannan farashin na litar man fetur Basu da wata riba sai Hasara Kuma gwamnatin tasan da Hakan .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *