Hukumar lafiya ta duniya: “An samu matukar raguwar cutar mashaƙo, amma kuma cutar ta sake karuwa a baya-bayan”.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce an samu matukar raguwar cutar mashaƙo, amma kuma cutar ta sake karuwa a baya-bayan nan.

Cutar ta fi tsanani a kan yara da manyan da basu da allurar rigakafinta, domin yawan yin rigakafin ne ya sa cutar ta ragu sosai a tsakanin shekarun 1980 zuwa 2021, a duniya.

Sai dai a shekarar 2019, cutar mashako da ake kira Diphtheria a likitance ta kama sama da mutane 20, 000.

Najerya, kasar da ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afrika, ta fuskanci barkewar cutar tun a watan Oktobar shekarar 2022.

Kuma tun bayan bullar cutar zuwa watan Janairun 2023, mutane 38 ne aka tabatar sun mutu a sanadiyyar cutar, a kasar.

Lamarin da likitoci ke dangantawa da rashin yin rigakafinta, wanda hakan ne kadai maganin cutar kawo yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *