Ganduje ya zargi Emefiele da kawo tsarin sauya fasalin takardun naira saboda rashin cimma muradinsa na samun takarar Shugaban kasa.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya zargi Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele da kawo tsarin sauya fasalin takardun naira saboda rashin cimma muradinsa na samun takarar Shugaban Kasa.

An dai yi ta alakanta Gwamnan na CBN da neman takarar Shugaban Kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC, lamarin da ya musanta bayan da wata kungiya ta biya farashin naira miliyan dari wajen saya masa takardun neman izinin shiga takara a jam’iyyar.

Da ya ke ganawa da manema labarai bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, Ganduje ya yi zargin Gwamnan CBN din ba ya son ganin Zaben 2023 ya wakana.

An dai shafe sa’o’i ana ganawa tsakanin Shugaban Kasa da gwamnonin APC, inda Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya yi zargin cewa akwai wadanda a Fadar Gwamnatin Najeriya da ke yi wa dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu zagon kasa don ya fadi zaben da ke tafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *