Gwamnan CBN Godwin Emefiele, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su nuna fahimta tare da cewa takardun da aka sake fasalin za su rika yawo kuma za a iya samun su.

Emefiele ya yi wannan roko ne a wani taron manema labarai a Legas na musamman kan sabbin kudaden musamman ganin yadda aka sami barkewar tarzoma da zanga zanga a wasu sassan Kasarnan saboda
Karancin Sabbin Takardun Kudaden Gwamnan babban bankin Najeriya ya roki ‘yan kasar da su ci gaba da
hakuri domin tuni su ka gana da shugabanin bankuna,an cimma fahimtar juna da nufin biyawa jama’a bukatun su cikin sauki.

Gwamnan babban bankin Najeriya ya dau alkawali tare da bayyana cewa za’a kawo karshen tsarin nan na takaita adadin kudin da ake iya cirewa, za a cire iyaka kuma mutane za su iya gudanar da harkokinsu na kasuwanci kamar yadda aka saba a baya.

Hakanan akan cajin da wakilan da ke gudanar harakokin su a POS ke yi kan duk wani ciniki da abokan cinikinsu, Emefile ya bukaci bankunan da su dakatar da cajin kan POS.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *