CBN Ya Bada Sabon Umarni Ga Bankuna Akan Sabbin takardun Naira

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan ajiya da su fara biyan kudaden da aka sauya wa fasali ta kan kanta, kuma ya bayyana Naira 20,000 a matsayin yawan kudin da mutum zai iya dauka a kowace rana.

Umurnin na zuwa ne daidai lokacin da karancin takardun da aka sauya wa fasalin ya jefa 'yan kasuwa cikin tashin hankali, yayin da suka ajiye duk tsofaffin takardun kudin dake hannunsu a asusun ajiyar su.

Babban bankin na CBN ya nanata kudurin sa ga ‘yan Najeriya na tabbatar da yadda ake rarraba sabbin takardun kudin Naira da aka sauya wa fasali, inda ya bukace su da su yi hakuri yayin da CBN ke bakin kokarinta wajen ganin ta magance kalubalen da ake samu na layukan ATM.

Sanarwar wacce Daraktan Sadarwa na Kamfanin, Osita Nwanisobi, ya sanya wa hannu, ta ce CBN ya lura da matukar damuwa, mutanen da ke sayar da sabbin takardun kudi da kuma wadanda ke cin zarafi da ka’ida ta hanyar liƙi ko tattaka naira a wuraren  bukukuwa 

Sun kuma jaddada cewa za su ci gaba da aiki da hadin gwiwar hukumomin FIRS, EFCC da NFIU domin maganin masu yin hakan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *