Emefiele Ya Bayyana A Gaban Majalisar Wakilai Batun Canjin Kudi

Bayan shafe tsawon lokaci ana kai ruwa rana a kan batun canjin kudi, daga karshe dai Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai.

Kwamitin dai ya gayyaci Gwamnan ne saboda rikita-rikitar da ta dabaibaye  batun canjin takardun kudin tun lokacin da wa’adin da banki.

Shugaban Kwamitin, kuma Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa ne aka dora wa alhakin jagorantar kwamitin don tattaunawa da CBN da sauran bankunan kasuwanci a kan batun.

Tun da farko dai kwamitin ya gayyaci Emefiele ne domin ya yi masa bayani a kan batutuwan da suka dabaibaye canjin, da kuma bukatar tsawaita wa’adin daina karbar tsoffin kudaden da a baya aka shirya yi a ranar 31 da watan Janairu.

To sai dai daga bisani, CBN ya kara kwana 10, inda wa’adin yanzu ya koma zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, domin ba ’yan Najeriya damar kai takardun kudadensu na N1,000 da N500 da kuma N200 zuwa bankuna.

Duk yadda zaman Gwamnan na CBN da kwamitin ya kaya, zai taka muhimmiyar rawa wajen ko za a sake kara wa’adin ko kuma a’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *