Adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar zazzabin Lassa a jihar Edo ya kai 13, yayin da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar sun kai 115 tun bayan bullar cutar a jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Akoria Obehi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Benin a ranar lahadi da ta gabata.
A cewarsa, gwamnati na kara kaimi wajen ganin an dakile cutar a fadin kananan hukumomin jihar.
“Mun samu karin mutane 8 da suka kamu da cutar, wadanda a halin yanzu ke samun kulawa a asibitin koyarwa na Irrua.”
Farfesa Akoria Obehi
Yayin da yake bayyana cewa a shirye jihar take kuma tana da isashen kayan aikin da za ta iya kula da masu kamuwa da cutar zazzabin Lassa, Farfesa Akoria, ya bukaci mutanen da suka kamu da wata rashin lafiya kamar ciwon kai mai tsanani, amai, da zazzabi, da sauran su garzaya wurin kula da lafiya mafi kusa domin samun magani.