Babban bankin Njaeriya CBN ya tsawaita wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun Naira zuwa 10 ga Fabrairu 2023
Gwamnan babban bankin kasar CBN, Godwin Emefiele ne ya sanar da karin wa’adin a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Lahadi 29 ga watan Junairu, 2023.
Hakan na zuwa ne bayan da ‘yan Najeriya suka yi kira da a kara wa’adin, duba da karancin sabbin takardun.
Tun da farko dai gwamnan na CBN ya dage cewa ba za a kara tsawaita wa’adin ba, yana mai cewa sace mutane da karbar kudin fansa sun ragu tun bayan da aka sake fasalin takardun kudi guda uku.
Ya kuma ce lokacin da aka bayar na musanya tsofaffin takardun kudi na Naira da sababbi ya isa ‘yan Najeriya suje bankunan su karbi sabbin takardun kudi.