An kara samun matsin lamba ga Babban Bankin Najeriya (CBN) kan ya kara wa’adin ranar 31 ga watan Janairu na janye tsofaffin takardun kudi na N1,000, N500 da N200. Su ma masu ruwa da tsakin sun ce wa’adin ba zai yiwu ba saboda ba a samu sabbin takardun.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) da Kungiyar Kare Hakkokin Musulmi (MURIC) da dai sauransu, sun kara da cewa a tsawaita wa’adin ko a soke wannan manufa kai tsaye har sai kasar ta shirya.
Sun yi wannan kiran ne kwana 3 ya rage a wa’adin ranar 31 ga watan Junairu da bankin ta sanar, yayin da jama’a a fadin kasar nan ke kokawa kan halin da suke ciki na rashin samun damar cire takardun naira da aka yi wa gyaran fuska daga banki ko kuma naurorin ATM.
Rahotanni a ranar Asabar sunyi nuni da cewa tuni wasu marasa kishin kasa na babban bankin kasa CBN da kuma bankunan kasuwanci ke hada baki don siyar da sabbin takardun kudin ga masu nemansa.
Misali, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, masu satar kudi da ke zama a bakin bankuna suna karbar naira 11,000 na tsofaffin takardun kudi a madadin N10,000 na sabbin.
Haka lamarin yake a Kano inda ake zargin wasu jami’an CBN sun dauki sabbin takardun naira zuwa masallatai da coci-coci daban-daban domin rabawa ma’aikatan POS, inda su kuma za su raba kudin ga ‘yan kasa da ke cikin halin kaka-nika-yi da suke son cirewa tsohon takardunsu.
Daya daga cikin ma’aikatan POS mai suna Kabiru Isiaku ya ce, “An bukaci mu je masallacin da ke unguwarmu a Hotoro, kuma ni ne na farko da muka fara zuwa wurin.
“An gaya mana cewa za su zo da Naira miliyan 10 don raba mana. Muka jira har kusan azahar. Kuma da suka raba kusan Naira 700,000, sai suka ce mu je masallaci mu dawo daga baya; Da muka dawo sai muka gano sun tafi. Duk abin da ake yi na rake ne,” inji shi.
Wata ‘yar kasuwa a garin Hadejia da ke Jihar Jigawa, Sajo Aliyu, ta ce, “Hakan ya sabawa abin da ake tsammani. Tabbas sun zo da wani abu kamar bankin wayar hannu don musanya kuɗaɗe, amma idan ka je da N300,000 sai su ba ka N10,000 na sababbin kuɗi kawai su bar maka N290,000 na tsofaffin takardun kudi. Ban fahimci abin da ke faruwa ba,” in ji shi.