KEDCO Ya Shawarci Abokan Huldarsa Kan Karancin Sabbin Kudade

Yayin da wa’adin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya diba na daina amfani da tsoffin takardun Naira ya kusa cika, Kamfanin Rarraba Hasken Wutar Lantarki na Shiyyar Kano (KEDCO) ya shawarci abokan huldarsa kan yin amfani da wasu hanyoyin wajen biyan kudin wuta.

Hakan, a cewar kamfanin zai taimaka wajen saukaka wa mutane a jihohin da yake aiki su yi maganin kalubalen bin dogayen layuka a bankuna domin cire kudaden da za su biya kudin wuta ko na mita.

KEDCO a cikin wata sanarwa da Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na kamfanin, Sani Bala Sani, ya fitar ranar Alhamis, ya ce mutane za su iya amfani da wasu hanyoyin da suke aiki ba dare ba rana.

A cewar sanarwar, “Mun dauki matakin ne don saukaka wa mutane irin halin da za su shiga wajen bin matakin CBN na rage amfani da tsabar kudi.

“Daga cikin hanyoyin da za a iya amfani da su a madadin haka akwai ta hanyar amfan da sahfin kamfanin a intanet da kuma ta hanyar danna *389*16*lambar mita# a waya, da dai sauransu.

“Muna bayar da tabbacin cewa da zarar mutum ya yi amfani da wadannan hanyoyin, zai samu rasidinsa na biyan kudi nan take,” in ji sanarwar.

Kamfanin ya kuma ce ya fito da wani tsarin garabasa da rangwamen kaso 25 cikin 100 ga abokan huldarsa da suka biya basukan da ake binsu da tsoffin takardun N200 da N500 da kuma N1,000, daga yanzu har zuwa 30 ga watan Janairu.

KEDCO ya kuma shawarci abokan huldar tasa da su yi amfani da lokacin garabasar na kwana biyar wajen biyan basukan da ake bin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *