Gwamnatin Jihar Bauchi ta raba shanu, raguna da kuma kayan abinci na sama da Naira miliyan 145 ga kiristoci da ke jihar

Gwamnatin Jihar Bauchi ta raba shanu, raguna da kuma kayan abinci na sama da Naira miliyan 145 ga kiristoci da ke jihar don gudanar da shagulgulan bikin Kirisimeti cikin annashuwa da walwala.

Shugaban kwamitin rabon kayan kuma mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin ma’aikata, Mista Abdon Dalla Gin, shin ya shaida hakan ga manema labarai yayin kaddamar da rabon a ranar Juma’a.

Haka nan shugaban kwamitin ya ce sun yi tsari mai kyau yayin rabon ta yadda dukkan bangarorin kungiyoyi da majami’u da su ke jihar za su amfana da tallafin ba tare da nuna wariya ga kowane bangare ba.

Wasu daga cikin wakilan kungiyoyi da Majami’u da su ka karbi tallafin sun yi godiya ga gwamnan jihar, bisa tallafa musu da ya ke don samun sauki wajen gudanar da bukukuwan kirsimeti kowace shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *