Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace ba zaiyi kewar Mulkin Najeriya ba tunda Yan kasa basuga kokarinsa ba saima kusheshi da akayi .

Buhari ya bayyana hakan ne a liyafar da ’yan uwa da abokan arziki suka sirya masa don taya shi murnar cikarsa shekaru 80 da haihuwa a Abuja, inda ya ce ’yan Najeriya na raina duk fadi tashin da yake kan
Najeriya don haka ba zai yi kewar mulkar ta ba idan wa’adin mulkinsa ya cika.

Da yake amsa tambayar ’yan jarida kan jita-jtar da ake yadawa cewa ba shi ne Buharin da ’yan kasar suka sani a baya ba, Buhari ya ce yana sane da hakan, sai dai sanin cewa ’yan Najeriya mutane ne masu son
raha ya sa bai damu ba.

Ya ce wannan batu ba abin dariya ba ne saboda wasu ne ke kokarin amfani da hakan don kau da hankalin ’yan Najeriya daga kan abubuwan da suke da muhimmaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *