Ma’aikatar aikin noma da raya karkara ta ce tana son a noma shinkafa ‘yar gida tan miliyan 34 a kakar noman shekarar 2023.

Wannan adadin da ma’aikatar ta sanar na kunshe ne a cikin sabon tsarin bunkasa noman shinkafa na kasa daga shekarar 2022 zuwa shekarar 2023 wanda ma’aikatar ta kaddamar a kwanan baya.

Tsarin dai na son ya cim ma burin kara habaka noman na shinkafar da sarrafa ta a kasar nan ta hanyar yin amfani da kayan aikin noma na zamani.

Bugu da kari, sanarwar ta kuma kara dacewa gwamnatin tarayya na son a yi renonon irin shinkafar tan tan 5,327 inda kuma za a samar da ingancin Irin shinkafar kashi 80 a cikin dari.

Tsarin wanda aka kaddamar da shi a birnin tarayyar Abuja, a jawabinsa a wajen kaddamarwar, karamin minista a ma’aikatar aikin noma da raya karkara Mustapha Baba Shehuri ya bayyana cewa, tsarin zai taimaka wajen a samar da alkibla domin a kara bunkasa noman shinkafar a kasar nan tare da wadata Najeriya da shinkafar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *