‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya su na shirin yaƙi da dokar cirar kuɗi da CBN ya bullo da ita.

‘Yan Majalisar Wakilan Najeriya su na shirin yaƙi da dokar cirar kuɗi da babban banki CBN ya bullo da ita duk da bankin ya kara adadin kudin da za a iya cirewa a kowacce rana.

Wasu ‘yan Majalisar Wakilan Najeriya sun ci alwashin tilasata wa Babban Bankin ƙasar (CBN) wajen dakatar da shirinsa na rage yawan adadin kudin da ‘yan ƙasa da kamfanoni kan cira a kullum.

Wani daga cikin shugabanni a Majalisar ya faɗa wa manema labarai cewa akasarinsu sun aminta cewa ya kamata a jingine dokar baki ɗayanta.

A cikin sabuwar dokar, mafi yawan abin da mutum zai iya cirewa a mako na tsabar kuɗi shi ne naira N100,000, kamfani kuma N500,000. Daga baya aka ƙara ya zama N500,000 ga mutane da kuma 5,000,000.

Tun da farko Majalisar ta nemi CBN ya jinkirta fara amfani da dokar tukunna, wadda za ta fara aiki daga 9 ga watan Janairun 2023, har sai gwamnan bankin Godwin Emefiele ya bayyana a gabanta.

Sai dai Mista Emefiele bai amsa gayyatar ba yana mai cewa ya fita ƙasar waje don a duba lafiyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *