Fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ne su ka tsunduma cikin duhun rashin hasken lantarki, sannan an soke tashin dubban jiragen sama a ranar Juma’a.
Aƙalla mutum 12 aka tabbatar sun mutu sanadin matsanancin sanyin a sassan ƙasar.
A Kanada ma, biranen Ontario da Quebec na fama da muku-mukun sanyin ƙanƙara da ya janyo katsewar wutar lantarki ga dubban gidaje.