Kamfanin haƙar ɗanyen man fetur na Shell zai biya diyyar dala miliyan 16 ga wasu manoma a yankin Neja-Delta da ke a kudancin Najeriya.

Hakan na cikin diyyar da kamfani zai biya ga waɗanda malalar man fetur ta yi musu barna a gonakinsu.
Alƙawarin biyan diyyar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a tare da haɗin gwiwar reshen cibiyar Friends of the Earth da ke a ƙasar Netherlands.

Matakin ya biyo bayan hukuncin kotun Netherlands inda ta kama reshen amfanin na Shell a Najeriya da laifin malalar mai a shekarar da ta gabata kuma ta umarci Shell ya biya diyya

Tun a shekarar 2008 ne manoma daga Neja-Delta tare da taimakon kungiyar kare hakkin bil adama ta Friends of the Earth su ka gurfanar da Shell a gaban kotun da ke birnin Hague sakamakon gurɓata musu muhalli da ya yi a tsawon shekarun da ya shafe ya na haƙo albarkatun fetur a yankin.

Kamfanin Shell ya yi barnar a shekarun 2004 zuwa 2007. Kuma a cewarsu malalar ta hanasu noma gonakinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *