Jagorar tawagar da ma’aikatar ta tura Katsina domin wayar da kan jama’ dangane da shirin wato Nadia Muhammad ce ta bayyana hakan.
Inda ta ce aikin tantance sunayen wanda ake gudanarwa a ƙarƙashin Ma’aikatar Ayyukan Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa wadda Minista Sadiya Farouk ke Jagoranta zai ɗauki sunayen ne daga ƙananan hukumomi 11 domin su shiga cikin tsarin masu cin gajiyar shirye-shiryen da ma’aikatar ke samar wa masu bukatar agajin gaggawa a faɗin ƙasar nan.
Nadia Muhammad ta ce za a sa ka sunayen waɗanda za a tantance a shirin bayar da tallafin kuɗaɗe ga mabukata na musamman da shirin bayar da jarin tallafawa a yi ƙananan sana’o’i, da shirin N-Power, da shirin ciyar da ɗalibai da dai sauran su.
Wasu da hareharen ‘Yan bindigar ya shafa daga kananan hukumomin Jibia, da Batsari da Kurfi, sun shaida wa jami’an shirin cewa su na buƙatar muhallin zama.