Sojin Najeriya: “Muna Binciken Kisan Fararen Hula Harin Jiragen Yaki A Zamfara “.

Zamfara – Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce ta fara bincike kan zargin kisan fararen hula a luguden wuta da jiragen yaki suka kai kan ’yan ta’adda a Jihar Zamfara.

Daraktan Yada Labarai na Hedikwaar Tsaro, Manjo-Janar Musa Danmadami, ya ce hadafin harin jiragen yakin na ranar Lahadi shi ne dandazon ’yan bindiga da suka kai hari bisa babura a kauyen Mutumji da ke Karamar Hukumar Maru ta jihar.

“Mun kaddamar da bincike domin tabbatar da gaskiyar rasuwar fararen hula da abin ya ritsa da su, da kuma yawansu.

“A halin yanzu ba za mu iya cewa ga adadin ba, domin kada mu kawo cikas ga binciken da ke gudana.

“Jiragen sun yi luguden wutan ne kai-tsaye a kan ’yan ta’adda kuma an hallaka da dama daga cikinsu,” in ji shi.

Sai dai rahotanni daga jihar sun cewa fararen hula 60 sun mutu a sakamakon luguden wuta da jiragen yakin suka yi.

A kan haka ne Manjo-Janar Danmadami ya shaida wa ’yan jarida a ranar Alhamis cewa Hedikwatar Tsaro ta kafa kwamitin bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.

Amma ya ce har yanzu ba su samu wata sanarwa ko alkaluman fararen hulan da rahotannin ke cewa jiragen yakin sun kashe ba daga Gwamnatin Jihar Zamfara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *