Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya bayyana aniyar gwamnatinsa na inganta aiki da rayuwar ‘yan sandan Najeriya.

A Sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a Abuja, lokacin da ya karbi rahoto kan rundunar ‘yan sandan kasar na shekarar 2021, da karbar kudurin kasafin kudin ‘yan sanda na badi.

Ya kara da da cewa yasan duk lokutan da aka yi wa jami’an tsaro sauyin wurin aiki, baza suyi dar ba wajen zuwa aikin, saboda sanin sun bar iyalansu cikin ingantaccen muhalli.

Batun karawa ‘yan sanda albashi da walwala ya dade ana tattaunawa a kai a Najeriya, rashin samun albashi da alawus mai tsoka na daga cikin dalilan da ake cewa ya janyo kananan ‘yan sanda karbar na goro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *