Mista Abdullahi Aliyu-Yar’adua, Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Muntari Lawal ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Alhamis a Katsina.
“Nadin ya dogara ne akan ikon da aka baiwa gwamna ta tanadin jadawalin farko na kafa dokar Jami’ar mai lamba 7 na 2006,” inji shi.
Aliyu-Yar’adua ya kara da cewa, an nada Ida ne bisa la’akari da irin halayen shi na yi wa al’umma hidima da kuma gwamnati da al’ummar jihar.
Ya ce: “Gwamnan ya bayyana fatansa na cewa sabon shugaban jami’ar zai kawo hankalinsa na aiki da kuma dimbin gogewar da yake da shi a wannan sabon aiki domin ci gaban jami’ar baki daya.
“Masari ya kuma taya Ida murna tare da yi masa fatan alkhairi a wannan sabon nadin.” (NAN)