Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ne ya bada hujjar cewar ba zasu iya zartar da
kasafin kudin shekara 2023 ba.
Lawan ya ce kudurin Kasafin Kudin ya zowa da Majalisar ne da wasu matsaloli da kwamitocin Majalisar dattawa da ta Wakilai suka gano a lokacin da suke daidaita alkaluman abinda akayi da kuma abinda aka gabatar wa majalisar.
Lawan ya ce matsalolin basu da sauki kuma dole ne kwamitocin su tsaftace lissafin kafin a zartar da kasafin, sai dai bai bada cikakken bayani kan irin matsalolin da aka gano a kasafin ba.