Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar, Hussain Ali Kila, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce gwamnatin za ta rarrabawa masu ruwa da tsaki sanarwar amfani da sabuwar dokar, domin fara aiwatarwa daga watan Janairun 2023.
Kafin sabon tsarin dai, ana biyan ’yan fanshon N5,000 ne a matsayin mafi karancin albashi.