Kotu Ta Tabbatar Da Abacha A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Jam’iyyar PDP

Babban kotun tarayya da ke zamanta a Kano, a ranar Alhamis, ta tabbatar da Mohammed Sani Abacha, a matsayin halastacen zababben dan takarar gwamna na PDP a jihar Kano.

A hukuncinsa, a yammacin ranar Alhami, Mai sharia A.M. Liman ya soke zaben cikin gida da jam’iyyar ta yi inda Sadik Aminu Wali ya yi nasara.

KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin tarayya ta ce ba za ta iya kammala aikin shimfida layin dogo na jirgin ƙasa wanda zai hada gabashin ƙasar nan da kudanci ba kafin ƙarewar wa’adin mulkin Buhari.

Da farko an shirya yin hukuncin ne da karfe 12.00 na rana a ranar Alhamis amma daga baya aka matsar da shi zuwa karfe 4.00 na yamma kuma aka bayar da shi da misalin karfe 5.30 na yamma. Kotun ta amsa dukkan bukatun da mai shigar da kara ya nema a masa.

Wanda ya shigar da karar shine Mohammed Sani Abacha, yayin da wanda aka yi kara na farko itace hukumar INEC.

Sarki Aminu Wali shine wanda aka yi kara na biyu, yayin da jam’iyyar PDP ce ta uku sai kuma Wada Sagagi shine na hudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *