Gwamnatin tarayya ta nuna bakin cikinta da damuwarta kan rasa rayuka da aka samu a karamar hukumar mulki ta maru.

Gwamnatin tarayya ta nuna bakin cikinta da damuwarta kan rasa rayuka da aka samu a karamar hukumar mulki ta maru, bisa wani hari da sojojin kasar nan suka kai ta jirgin yaki.

Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai yaran kauyuka da dama wanda suke kewaye da juna da suka rasa ransu sabida kai harin.

Tun da fari dakarun sojin sunce su auna iya inda ”yan bindigar suke, amma daga bisani ‘yan bindigar suka shiga cikin kauyukan.

Yayin zantawarsa da manema labarai, ministan labarai da al’adu Lai Muhammad yace gwamnati ta dau alhakin wannan al’amari.

Lai Muhammad Ya ci gaba da cewa yanayin yaki ne haka, duk da yadda sojoji suke kula dole ne za’a samu sabani, musamman ma tunda niyyarsu ita ce kawo karshen wannan matsalar tsaron data damu kowa.

Hukumomin sojin sama ma sun bada hakuri kan wannan abinda ya faru, suna cewa sun aikata ne bisa rashin sani ko ajizanci na dan adam da ba makawa watara sai ya hadu dashi ko kuma ya aikatashi bai sani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *