Gwamnatin tarayya ta ce ba za ta iya kammala aikin shimfida layin dogo na jirgin ƙasa da ta ce za ta yi da zai hada gabashin ƙasar da kudancin ƙasar ba, kafin ƙarewar wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.
Gwamnatin ta ce kammala aikin shimfada layin dogon ba abu ne mai yiwuwa ba saboda
ƙarancin kudaden da za a yi aikin.
Ministan harkokin sufurin ƙasar, Mu’azu Jaji Sambo, ne ya sanar da hakan bayan kammala zaman majalisar zartarwar ƙasar da ya gudana a ranar Laraba.
A cewar sa gwamnatin tarayyar, ba ta sami damar karbar kudin hadin guiwar da za a gudanar da aikin ba, wanda hakan ya sa suka gaza samar da kudaden da suka kamata a yi aikin.
Jihohin da za su ci gajiyar aikin sun haɗa da jihohin Ribas, Abia, Anambra, Imo, Ebonyi da Enugu, da Nasarawa, Benue, Plateau, Kaduna, Yobe, Borno, Bauchi da kuma Gombe.
Shekara biyu da suka gabata ne, tsohon ministan Sufurin Najeriya Rotimi Amaechi, ya ce za a kammala aikin shimfida layin dogon na Fatakwal zuwa Maiduguri kafin karewar mulkin Shugaba Buhari.