NDLEA: “Cikin watanni 22 da suka gabata munyi nasarar kwato kwayoyin Tramadol da wasu haramtattun kwayoyi na sama da miliyan 100′.

Hukumar dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta bayyana cewa, cikin watanni 22 da suka gabata hukumar ta yi nasarar kwato fiye da kwayoyin Tramadol sama da miliyan dari da wasu tarin haramtattun kwayoyi wadanda ke illata rayuwar matasa da cigaban Najeriya.

Shugaban hukumar ta NDLEA, Burgediya janar Buba Marwa ne ya bayyana hakan yayin taron bikin karshen shekara ta 2022, inda aka karrama wasu daga cikin jami’an da suka nuna hazaka da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu mabanbanta tare da kara musu girma a hukumar inda ya ce an yi nasarar kama masu safarar miyagun kwayoyi dubu 23,907 ciki har da gungun masu sayar da kwayoyi su 29.

Kazalika an kama fiye da ton dubu 5,500 na haramtattun kwayoyi wadanda idan aka hada harda kudaden da aka kama jimillar su zai kai sama da Naira biliyan 450.

Burgediya janar Buba Marwa ya danganta wannan nasara da hukumarsa ta samu bisa ga gudumawar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar ga aikin hukumar na dakile yaduwar miyagun kwayoyi a kasar da kuma jajircewa jami’an hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *