Majalisar dokokin Kano ta gabatar da kudiri dake neman samar da kulawa da lafiyar mata da kananan yara a kyauta

Majalisar dokokin Kano ta gabatar da kudiri dake neman yin doka da zata rinka kulawa da mata masu ciki da kananan yara kyauta

Jaridar Rahma ta ruwaito cewa makasudin wannan kudurin shine, don basu kulawa a asibitoci jihar ba tare da sun biya ba.

Dan majalisa mai wakiltar Rogo, Magaji Dahiru Zarewa, da hadin gwiwar dan majalisa mai wakiltar Takai, Musa Ali Kachako, ne suka gabatar da kudirin a zaman majalisar a Talatar nan.

Da yake jawabi a gaban majalisar, Magaji Dahiru Zarewa, ya ce idan aka amince da kudirin ya zama doka zai magance matsalar mace-macen yara da ake samu da kuma kulawa da mata tun daga daukar ciki zuwa haihuwa.

Yanzu haka dai ana ci gaba da samun mutuwar mata masu juna biyu, sakamakon rashin samun kulawar da ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *