Kotun Burtaniya Ta Sake Hana Ekweremadu Beli.

Kotun hukunta manyan laifuka ta Landan da aka fi sani da Old Bailey ta sake hana beli ga tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu.

A zaman da kotun tayi a ranar Talata, kotun ta yanke hukuncin kin amince da belinsa ne bisa hujjar cewa zai iya tserewa.

Kotun ta bayar da misali da wasikar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta’annati da bincike Sanatan har ma da kwace wasu daga cikin Kadarorin sa da ya mallaka.

KARANTA WANNAN LABARIN: Kasar Ingila ta yi sabon kudi mai dauke da hoton sabon Sarki Charles

Lauyan nasa ya ce an bayar da tabbacin cewa za a dawo da shi idan har ya gudu daga kasar.

Haka kuma ofishin jakadancin Najeriya a Birtaniya ya ba da damar sanya wa wata na’urar bibiya ga Ekweremadu don sa ido kan motsin sa.

Da yake magana game da shaidar halayen Ekweremadu da ‘yan Najeriya masu daraja da kungiyoyi suka yi, lauyansa ya kuma ce ya tabbatar da cewa Ekweremadu uba mai kulawa kuma ba zai iya tserewa daga Landan ba, ya bar matarsa ​​da ‘yarsa mara lafiya.

Lauyan ya kuma shaida wa kotun cewa suna da shaidu na kusan rabin fam miliyan daga mutane 11 domin a ba da belin Ekweremadu.

Da yake bayyana cewa Ekweremadu mutum ne da ake girmamawa, kuma sananne ga jama’a, Lauyan nasa ya kuma yi nuni da yadda Ekweremadu ya shiga cikin jerin wadanda yi ayyukan na jin kai a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *