INEC ta ce tana bukatar motoci 100,000 da kwalekwale 4,200 saboda jigilar ma’aikata da kayan zabe a babban zaben 2023.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce tana bukatar motoci 100,000 da kwalekwale 4,200 saboda jigilar ma’aikata da kayan zabe yayin babban zaben 2023.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan yayin sanya hannu a kan wata yarjejeniya tsakanin kungiyar direbobi ta kasa da takwararta ta masu tuka kwalekwale a Abuja.

Shugaban na INEC ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa na cewa mambobin kungiyoyin biyu zasu tabbatar da mambobinsu sun bayar da cikakken hadin kai yayin aikin.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW), Alhaji Tajudeen Baruwa, ya ce a shirye suke wajen ganin an gudanar da zaben cikin nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *