CBN Ya Kara Adadin Kudaden Da ’Yan Najeriya Za Su Iya Cire Duk Sati

Sanarwar da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar a ranar laraba ya bayyana cewa bankin ya kara adadin tsabar kudi da ‘yan Najeriya za su iya cirewa a asusun banki duk mako zuwa N500,000, yayin da kamfanoni za su iya cire Naira miliyan 5 duk mako.

Wannan karin na zuwa ne a cikin wata wasika da CBN ya aikewa dukkan bankunan kasar nan a ranar Laraba 21 ga watan Disamba.

Babban bankin ya yanke wannan shawarin ne bayan sauraran korafe-korafe daga daga masu ruwa da tsaki a Najeriya.

Ga mutanen da suke sha’awar cire sama da N500,000, CBN ya basu damar hakan, amma za su biya kasho 3% na kudin da suke son cirewa.

Hakazalika ga kamfanonin da ke son cire sama da N5m, za su biya kashi 5% na adadin kudin da suke son cirewa, kamar yadda yazo a sanarwar da muka samo. A bangare guda, bankuna ba za su ke biyan cekin da aka ba wani ba da ya haura N100,000, sabanin yadda dokar baya ta kayyade da N50,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *