Buhari Ya Amince Ya Taya Tinubu Yakin Neman Zaɓe

Fadar shugaban kasa ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince zai yi taya dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu da sauran ‘yan takarar jam’iyyar yakin neman zabe.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Garba Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Laraba.

Shehu ya ce Shugaba Buhari a shirye yake ya yiwa Tinubu da duk ‘yan takarar jam’iyyar APC yakin neman zabe da karfin gaske.

Wannan alwashi dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar bai fito a yakin neman zabe ba tun bayan kaddamar da na kasa a garin Jos na jihar Filato a tsakiyar watan Nuwamba.

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce yayin da Buhari ke ci gaba da jajircewa kan siyasar jam’iyya, ayyuka da ayyukan shugaban kasa za su kasance a kan gaba.

Da take tsokaci kan kalaman shugaban kasar ga al’ummar Najeriya mazauna birnin Washington DC a ziyarar da ya kai kasar Amurka kwanan nan, fadar shugaban kasar ta ce Buhari “a shirye yake ya yi yakin neman zaben jam’iyyar a babban zabe mai zuwa a shekara 2023

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *