NEMSA: Ayyukan wutar lantarki guda 10,692 ne daga cikin 15,931 da aka gudanar aka tabbatar da ingancinsu a harkar wutar lantarkin kasar nan.

Gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya, NEMSA, ta ce ayyukan wutar lantarki guda 10,692 ne kawai daga cikin 15,931 da aka gudanar aka tabbatar da ingancinsu a harkar wutar lantarkin kasar nan.

Manajan Daraktan NEMSA, Aliyu Tahir ne ya bayyana hakan ga manema labarai inda ya ce ana bukatar aiwatar da aikin dubawa da ba da takardar shaida domin dakile hadurran da ke tattare da yin amfani da wutar lantarki ta hanyar da bata dace ba, wanda ke haifar da raunuka, da asarar rayuka, da kuma lalata dukiyoyi.

KARANTA WANNAN LABARIN: KASTLEA ta ce za ta fara sakin dukkan baburan da aka kama ga mamallakansu daga Talata.

A cewarsa, hukumar ta sanya ido kan na’urorin samar da wutar lantarki 12,114 a fadin kasar.

Ya ce:

“Binciken ayyukan samar da wutar lantarki sama da 15,931 a fadin kasar nan, daga cikinsu 10,692 sun samu shaidar cancantar amfani da su ta NEMSA.”

Aliyu Tahir, Manajan Daraktan NEMSA

Ya kara da cewa NEMSA ta duba sama da na’urorin lantarki 3,255 a masana’antu da gine-gine wadanda suke hadari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *